Matafiya na cikin zulumi a Senegal saboda rashin jirage
March 17, 2020Talla
Gwamnatin ta Senegal ta dau wannan matakin na dakatar da zirga-zirga jiragen sama tsakaninta da kasashen Faransa da Italiya da Portugal da Beljiyam da Tunisiya da kuma Aljeriya domin dakile yaduwar cutar Coronavirus. Ministan sufiri na kasar Alioun Sarr ya ce dokar za ta yi kwanaki 30 tana aiki har sai al'amura sun fara daidaita. Senegal na daga cikin kasashen Afirka inda cutar ta Coronavirus ta bayyana wanda kawo yanzu ake da kusan mutane 27 da suka kamu da ita.