An garkame birnin Dakar
January 6, 2021Talla
Watanni shida bayan da kasar ta fita daga dokokin hana zirga-zirga, Shugaba Macky Sall na Senegal ya sake garkame kasar farawa daga yau Laraba, a wani mataki na yaki da bazuwar kwayar cutar Corona.
Hukumomin lafiyar kasar ta Senegal sun bayyana sake barkewar cutar ne bayan kammala bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara.
Dokar za ta shafi yankunan Dakar da kuma Thies inda abin ya fi kamari. Matakan da aka dauka sun hada da tilasta amfani da takunkumi da kuma hana zirga-zirga daga karfe 9 na yamma zuwa 5 na safe.
Kimanin mutane 19, 964 ne suka kamu da cutar kawo yanzu, yayin da 428 cutar ta hallaka a kasar.