1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Senegal ta ce dakarunta za su cigaba da zama Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
August 19, 2022

Ma'aikatar tsaron kasar Sénégal ta musanta kalamun cewa za ta kwashe dakarunta da ke aikin tabbatar da tsaro a karkashin inuwar rundunar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali.

https://p.dw.com/p/4Fmy9
Mali | MINUSMA | Friedenstruppen | UNPOL
Hoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/IMAGO

Rundunar tsaron Senegal ta jaddada matsayinta na cigaba da aiki kafada-da-kafada da rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali Minusma, a wani mataki na mayar da martani kan wani cece-kucen da ya barke, bayan madugun 'yan adawar kasar Ousmane Sonko ya zargi Senegal da kwashe dakarunta.

Mista Sonko da ke jawabi a yayin wani bikin tsayar da a takarar shugabancin kasa, ya zargi shugaba Macky Sall da zama dan amshin shatan Faransa, yana mai cewa tun fil-Azal dakarun Senegal na Mali ne kurum don gam da bukatar Faransa, ba wai don taimakawa 'yan Mali fita daga kangi ba, kalamun da ma'aikatar tsaron Senegal ta musanta.

Ita da Senegal tamkar wasu sauran kasashen duniya na da jami'an tsaro 1.300 ne karkshin inuwar rundunar Minusma a Mali, tun bayan da rikicin ta'addanci ya barke tare da daidaita wannan kasa da ke yankin yammacin Afirka.