Senegal za ta tusa ƙeyar tsohon shugaban ƙasar Cadi zuwa ƙasar sa
July 8, 2011Talla
Shugaban ƙasar Senegal Abdulaye wade ya yanke shawarar tusa ƙeyar tsohon shugaban ƙasar Cadi Hissène Habré zuwa ƙasarsa ta asili.Sanarwar wacce gwamnatin ƙasar Cadi ta baiyana, ta ce za a turo tsohon shugaban ne a cikin wani tashin jirgin sama na musammun a ranar Litini mai zuwa idan allah ya kai mu.
Habre wanda ya jagoranci ƙasar Cadi daga shekara ta 1982 zuwa shekara ta 1990 wanda kuma ya ke zaman gudun hijira a Senegal tun daga wannan lokaci.Ana tuhumar sa da laifin keta hadin bil adama da kuma aikata gisan gila akan daruruwan jama'a
Mawallafi : Abdorahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu