An fara zaben shugaban kasa a Senegal
February 24, 2019Akalla mutun miliyan shida ne na 'yan kasar Senegal ke shirin kada kuri'a domin zaben shugaban kasar daga 'yan takarar biyar da ake fafatawa a zaben na bana. Shugaban kasar Macky Sall mai shekaru 56 na daga cikin 'yan takarar da ke neman wani sabon wa'adi na biyu na mulki.
Da sanyin safiyar yau Lahadi jama'a a cikin wani yanayi na tsaro sun yi tururuwa zuwa cibiyoyin zabe a kasar, wanda kuma kawo yanzu rahotanni ke cewa komai na tafiya a cikin tsanaki.
Ana gudanar da zaben ne ba tare da wasu 'yan adawa Karim Wade da Khalifa Sall ba, wadanda suka yi kaurin suna wajen caccakar gwamnatin Makcy Sall bisa zarginsu a baya da kotun kasar ta yi da aikata laifi na almundahana da dukiyar kasa.
Ana sa ran fara samun cikakken sakamakon zaben a ranakkun 25 zuwa 26 ga wannan wata.