Shakku a kan yaki da 'yan ta'addan IS
October 10, 2014Kawo yanzu dai an tabbatar da cewa mayakan na IS sun kwace akalla sama da kaso uku bisa hudu na garin na Kobani. Wannan dai ya sanya shakku dama aza ayar tambaya kan tasirin yakin taron dangi a kan kungiyar ta IS da Amirka ke jagoranta a kasashen Iraki da Siriya tun cikin watan Satumbar da ya gabata. A hannu guda kuma kasar Turkiya ta sanar da cewa abu ne da ba zai yiwu ba a tsammaci za ta kaddamar da hari ita kadai a kan iyakarta domin ta kare wani gari da ke zaman na Kurdawa kawai. Kawo yanzu dai Amirka da kawayenta da suka hadarda kasashe daga yankin Gabas ta Tsakiya sun yi barin bama-bamai ta hanyar kai hare-hare da jiragen sama fiye da sau 130 domin dakile ayyukan kungiyar ta IS.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu