Ziyarar Olaf Scholz a kasashen Afirka
May 25, 2022A cewar shugaban Sashen na Afirka Claus Stäcker dai, har yanzu ana ganin kimar Angela Merkel a Afirka. A Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar har, makarantar firamare aka gina da sunanta. Shahararta a nahiyar ta biyo bayan manufofinta kan 'yan gudun hijira a shekara ta 2015, tun daga lokacin ake wa Jamus kallon jaruma tsakanin kasashen Turai. Scholz dai ya yi nazari sosai kafin zabar kasashen da ya kai ziyarar a suka hadar da: Senegal kasancewar a yanzu ita ce ke rike da shugabancin kungiyar Tarayyar Afirka na karba-karba, kuma ke da karfin fada a ji a yankin. Jamhuriyar Nijar kuwa, daman abokiyar Jamus ce mai binta sau da kafa. Kana a matsayinta na kasa mai dogaro da kai, tana da rawar da za ta taka wajen ceto makwabciyarta Mali daga halin da take ciki.
Karin Bayani: Jamus za ta taimaka wa Nijar inji Scholz
A fannin tattalin arziki kuwa, Afirka ta Kudu na da tasiri ga kungiyar Kasashe ma su Karfin Tattalin Arziki ta G20 da ma cibiyar kamfanonin Jamus. Kasahen dai sun yabawa wannan ziyarar ta Scholz da ke zuwa watanni kalilan bayan darewarsa karagar mulki, sabanin wacce ya gada Angela Merkel da sai bayan shekaru biyu ta doshi Afirka. Ziyarar tasa dai na zuwa ne, a daidai lokacin da duniya ke cikin wadi na tsaka mai wuya. Shugaban gwamnatin na Jamus bai nufi Chaina ko Kuduncin Amirka ko kuma Ukraine ba, sai kawai ya nufi Afirka. Tabbas suna sane da bukatun Jamus a halin yanzu, kuma suna jin dadin sha'awar da Berlin ta nuna ba zato ba tsammani game da hanyoyin bututun mai a Afirka da ma'ajiyar iskar gas da tashar karkashin teku domin samar da tsabtataccen makashi wanda ba ya gurbata muhalli.
Wannan ne ya jagoranci tattaunawar gaba da gaba, wanda shi ne batun da ke mamaye duk wani taron bangarorin biyu na tsawon lokaci. Gabanin ziyara ta sa dai, tawagar ta Scholz ta nunar dac cewar akwai abubuwa da yawa da za su ji kuma ko shakka babu sun ji bukatu masu yawa. Girkewa da bayar da horo ga sojoji da samar da tashoshin wutar lantarki da hasken rana da hadin kai sakamakon annobar Corona da yaki. Batun kara taka muhimmiyar rawa a yammacin Afirka da kuma bai wa Afirka karin murya a cikin kungiyar G20. Jamus tare da Chaina da Rasha da Indiya da sauran masu fada aji dai, ba su kasance da muhimmanci ga Afirka ba. Sai dai kuma Afirka ta kasance mai muhimmanci sosai ga kasa kamar Jamus a bangaren samar da makamashi da tsaro, kana nan gaba a harkokin kasuwanci.
Karin Bayani: Huldar Jamus da Afirka za ta kara ingantuwa
Sai dai idan aka auna, har yanzu babu tabbas game da alkawuran na Scholz. Ya ambato batun dimukuradiyya da bin doka da oda, ayar tambayar a nan ita ce ko a yanzu Jamus za ta samar da 'yancin cin gashin kai a yammacin Afirka da manufofin Sahel bayan ficewar Faransa?. Kuma gayyatar da ya yi wa Senegal da Afirka ta Kudu zuwa taron kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya na G7 da za yi a Elmau, a halin yanzu wani abin farin ciki ne. Dangane da haka, Scholz dai zai dawo gida daga ziyarar Afirka tare da tarin darussa. Dangantaka da wannan makwabciyar nahiya na cikin wani yanayi saboda yakin Ukraine, amma kuma akwai damarmaki.