1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridu kan Angola da Zimbabuwe

Zainab Mohammed Abubakar
November 10, 2017

Jaridun Jamus a wannan makon sun shiga fagen siysar Zimbabuwe da kuma batun harkar man fetur da tattalin arziki a kasar Angola.

https://p.dw.com/p/2nQYr
Simbabwe Robert Mugabe mit Ehefrau Grace in Harare
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga labari kan yadda mulki ya zama  lamari na iyali a kasar Zimbabwe a wani labarin mai taken "Mugabe ya tsayar da martasa a matsayin magajiyarsa" da ta fidda. Wannan sharhi da jarida ta yi na zuwa ne daidai lokacin da shugaban kasar ya sauke mataimakinsa Emmerson Mnangagwa mai shekaru 72 da haihuwa daga kan mukaminsa tare da maye gurbinsa da mai dalinsa Grace mai shekaru 52 a wani mataki na sharar fage ne ga mai dakinsa kan batun gadonsa in ya bar mulki.

Ana kiran uwargidan Mugabe " Grace Gucci" saboda yadda ta ke da alaka da son kayan kawa na kamfanoni da suka yi suna a duniyar kwalliya. A matsayinta na tsohuwar sakatariyar shugaban kasar kafin ya aureta dai, Grace Mugabe ta jima ta na cin karenta babu babbaka ta irin rayuwar da ta ke gudanarwa na yawaita ziyartar manyan kasashen turai domin sayayyar kayayyakin da ta ke amfani da su. 

ANGOLA Verteidigungsminister João Lourenço (L)
Shugaba João Lourenço na AngolaHoto: Getty Images/AFP/A. Rogerio

To baya ga batun Zimbabuwe ma dai jaridun Jamus din sun tabo wasu batutuwa ciki kuwa har da abubuwan da ke faruwa a Angola. Jaridar Süddeutsche Zeitung alal misali ta wallafa wani sharhi mai taken "Har yanzu ba kowa ba ne ke cin moriyar arzikin kasa". A kasar Angola mai arzikin man petur har yanzu al'ummar kasar na rayuwa cikin talauci a yayin da arzikinta ke kara habaka tsakanin 'yan kasar kalilan masu jan akalar lamuranta.

Jaridar ta yi nazarin yadda 'yan Angolan ke cin gajiyar wata gidauniya daga ketare, daga albarkatun da ake fitarwa daga cikin kasarsu ta asali. Ta ba bada misalin wani ofishi da ake hada hadar lamuran da suka jibanci kasashen Afirka da dama wadda ke da matsuguni a birnin Geneva na kasar Switzerland.