1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhuna kan yaki da cin hanci a Tanzaniya

Zainab Mohammed AbubakarDecember 11, 2015

Hankalin jaridun na Jamus ya karkata kan yaki da cin hanci a Tanzaniya da belin Oscar Pistorius da neman hadin kan Afirka wajen kare kwararar 'yan gudun hijira Turai

https://p.dw.com/p/1HM9h
Tansania Präsident John Magufuli
Hoto: Getty Images/AFP/D. Hayduk

Jaridar Beliner Zeitung ta ce ta yaya za'a bayyana John Magufuli, a kirashi mai kawo sauyi a Afirka? ko kuma gwani??watanni biyu da suka gabata nedai aka zabi shi a matsayin shugaban kasat ta Tanzaniya, mai shekaru 56 da haihuwa kuma mutumin da a baya ake yi masa ikirari dakatapila sarkin aiki, sunan da ke da nasaba da irin ayyuka da ya yi a lokacin da yake kan mukamin ministan sufuri. Wata daya da hawansa wannan mukami dai tuni Magufuli ya yi kaurin suna ba wai a Afirka kadai ba har ma a idanun sauran kasashen duniya.

Magufuli dai ya fito a idanun duniya ne da ya soke bukin ranar samun 'yancin kan Tanzaniya, wadda acewarsa bai ga dalili bikin adai dai lokacin da mutane ke cigaba da mutuwa sakamakon cutar kwalera ba. A maimakon haka ne shugaban Tanzaniyan ya jagoranci aikin kwashe jujin da aka tara tare da share tituna a birnin Daressalam.

Itama jaridar Süddeutsche Zeitung bude sharhi ta yi akan shugaban kasar ta Tanzaniya mai taken "Katapila sarkin aiki" sabon shugaban kasar Tanzaniya ya na jagorancin gagarumin aikin yaki da cin hanci.

Südafrika Anhörung Oscar Pistorius
Hoto: Reuters/S. Sibeko

A ranar farko nsa na karbar karagar mulki dai Magufuli ya kai ziyarar ba zata zuwa ma'akatar kula da kudi, ziyarar da ta tsorata ma'aikata. A rana ta uku kuwa ya sanar da cewar baya ga shugaban gwamnati, babu wani babban jami'in gwamnati da ke ikon fita zuwa wata kasa ta ketare da sunan aiki, kasancewar akwai wasu muhimman batutuwa da ke bukatar a kashe musu irin wannan kudi fiye da tafiye tafiye babu hujja a bangaren jami'an gwamnati.

Daga watan Janairun shekara ta 2016 kuwa, yara zasu je makaranta kyauta har zuwa matsayin sakandare. A rana ta hudu ya kai ziyarar ba zata babban asibitin gwamnati na kasar, inda ya yi mamakin samun lalatattun nau'urori na bincike, a yayin da marasa lafiya ke kwance a kwaroron asibitin a kasa, nan take ya kori babban darektan asibitin tare da rusa hukumar gudanarwar.

Akan hukuncin da kotun daukaka kara ta sake zartarwa akan dan wasan rukunin nakasassun kasar Afirka ta Kudu Oscar Pistoriuskuwa jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung tsokaci ta yi dangane da matsayinsa na muradin hukuncin kotun kundin tsarin mulki. Jaridar ta ce, Pistorius mai shekaru 29 dai ya ki ya saduda. A ta bakin lauya da ke kareshi Barry Roux a babban kotun kasar a ranar Talata, fitaccen dan tseren nakasassun yana muradin daukaka wannan kara a kotun tsarin mulkin Afirka ta kudu.

Griechenland Flüchtling Tod bei Überfahrt
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Baltagiannis

An dai tabbatar da hukuncin kisa wadda zai kai Pistorius zaman wakafi na shekaru akalla 15, sai dai ana iya yin sassauci idan yanayin hakan ya lamunta. A yanzu haka dai ya samu beli daga kotun.

Za mu karkare sharhin jaridun na Jamus akan nahiyar ta Afirka sharhin da jaridar Die Welt ta yi kan ministar kula da muhalli ta Faransa ta yi na bukatar hadin kai da kasashen Afirka a siyasance domin magance matsalar. Segolene Royar da ke zama tsohuwar 'yar takarar kujerar shugabancin Faransa, ta yi amfani da taron sauyin yanayin Paris wajen jaddada bukatar wannan hadin kai tsakanin bangarorin domin gano bakin zaren warware matsalar.