1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
January 24, 2020

Zargin almubazzaranci da rashawa da ake wa 'yar shugaban kasar Angola Isabel dos Santos ne ya mamaye jaridun Jamus na wannan makon.

https://p.dw.com/p/3WlhD
'Yar shugaban kasar Angola Isabel dos Santos
Yar shugaban kasar Angola Isabel dos Santos Hoto: picture alliance/dpa/TASS/M. Metzel

Labarin mai taken "kudadden Jamus ga mace mafi arziki a Afirka, ya kwarmato bayanai a Luanda" na cewar, fiye da takardun bayanai dubu 700 ne ke bada haske game da mummunar kasuwanci ciki har da basussuka daga bankin Frankfurt da ke na Jamus. Sabbin bayanai da ba a wallafa ba, sun nuna yadda mace mafi arziki a nahiyar Afirkar, ta ninka dukiyarta da yawansu ya kai sama da dalar Amurka miliyan biyu. Isabel dai diya ce ga tsohon shugaba José Eduardo dos Santos, wanda ya yi mulkin kama karya a Angola mai arzikin man petur na kusan shekaru 40. 

Bugu da kari ta kuma samu tallafi daga kasashen ketare, ciki har da rancen kudi wajen euro miliyan 50, daga  wajen bankin Jamus a shekara ta 2015. Sai dai Isabel dos Santos ta musanta aikata duk wani laifi. Hadaddiyar cibiyar kwarmata bayanai ta Afirka ce dai ta samu sabbin bayanan tare da tawagar 'yan jarida na kasa da kasa masu bincike 120 daga kasashe 20, ciki har da Jamus.

Burkina Faso na fama da hare-haren 'yan ta'adda
Burkina Faso na fama da hare-haren 'yan ta'addaHoto: Imagao Images/ZUMA Press/A. Alcantar

"Kungiyoyin ta'adda na cigaba da tozarta al'umma" da haka ne jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta bude sharhinta kan halin kunci da Burkina Faso ta tsinci kanta a ciki sakamakon barazanar da kasar ke ciki. A ranar Talatar da ta gabata ne dai majalisar dokokin kasar ta yi wata sanarwar da ke neman hadin kan al'umma wajen kalubalantar 'yan ta'addan da ke ci gaba da zama kadangaren bakin tulu ga zaman lafiyar jama'a.

Sanarwar ta kara da cewar, cigaba da kai hari kan fararen hula ba wai yana bukatar matsa kaimi tsakanin jami'an tsaron kasar kadai ba, amma har da hadin kan jama'a. Don haka ne majalisar ta bada umurnin bada makamai ga duk wadanda keda niyyar shiga aikin tsaro na sakai. Ministan sadarwar Burkina Faso Remis Fulgance Dandjinou, ya sanar da cewar fararen hula 36 a kayi wa kisan kiyashi a wani hari da aka yankin arewacin kasar a wanbnan makon.