Sharhunan jaridun Jamus kan Afirka
May 24, 2019Bari mu fara da sharhin da jaridar Die Tageszeitung ta rubuta mai taken „tsallen murnar dawowar mai ceto: Katumbi ya koma Kwango.“ Bayan tsahon shekaru uku na neman mafaka, an kyale babban mai adawa da gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ya koma kasarsa. Garin Lubumbashi da ya fi tasiri na cikin rudani, yana ayyana kansa a matsayin jagoran adawa.
Ga mafi yawan al'ummar Katanga, Moise Katumbi mai ceto ne.
Jaridar ta ce: Duk wanda ke da sauran shakku kan samun sabuwar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a karkashin sabon shugaban kasa Félix Tshisekedi ya samu sabon tunani a ranar Litinin din da ta gabata. Dubun-dubatar mutane ne suka yi dafifi domin murnar dawowar babban jagoran adawar kasar Moise Katumbi. Hatta ma'aikatan filin jirgin saman kasar, sai da suka tafa masa yayin da jirginsa ya sauka a garin Lubumbashi da ke yankin kudancin kasar. Da yake jawabi ga manema labarai bayan saukarsa a jirgi, Katumbi mai shekaru 54 a duniya ya ce: "Na godewa Allah da ya dawo dani gida. Na zo domin tabbatar da zaman lafiya da kuma yin sulhu a tsakanin al'ummar kasarmu, abu mafi muhimmanci na kare muradun kasata da al'ummata. Na zo na ga 'yan uwana da suka jima suna shan wahala." Garin na Lubumbashi dai, shi ne cibiyar hakar ma'adinai na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kana babban birnin gundumar Katanga. Yayin da Katumbi tunanin tsayawa takara domin ya gaji Kabila a shekara ta 2015, ya rasa aikinsa kana aka tuhumeshi da daukar mayakan sunkuru da kuma mallakar fili ta haramtacciyar hanya. Ya tafi kasar Beljiyam, inda yana can aka yanke masa hukuncin zaman gidan kaso kana aka hana shi shiga takara a yayin zaben da ya gabata a shekara ta 2018. Bayan da Kabila ya mika mulki ga Tshisekedi cikin watan Janairu, an janye hukuncin kana an ba shi sabon fasfo da kuma kyaleshi ya dawo gida, shekaru uku cif bayan da ya yi gudun hijira. Ga mafi yawan al'ummar Katanga, Moise Katumbi mai mai ceto ne.
Kasar Mozambik na fuskantar matsin tattalin arzikin da ya janyo talauci a kasar
Talauci duk da dimbin arzikin albarkatun kasa, inji jaridar Neues Deutschland. Jaridar ta ce: Bayan afkawa cikin matsin tattalin arziki, Mozambik ta kasance tungar masu zuba jari. Sai dai tuni ta ake komawa gidan jiya kann batun matsin tatalin arzikin. Jaridar ta ce wani rahoto na hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ya nunar da cewa Mozambik na cikin kasashe 10 mafiya talauci a duniya. Kasar na fama da dinbin bashi kuma ayanzu tana cikin matsanancin hali, abin da ya sanya bukatar gaggauta sake ba ta agajin bashin. Mozambik dai ta karbi agajin bashin sama da dalar Amirka biliyan shida a ashekara ta 2001 da kuma 2005.
A Zimbabuwe 'yan siyasa na fuskantar bita da kuli daga wadandda uke gudanar da mulki
Za mu karkare da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta rubuta sharhinta mai taken:" A Zimbabuwe duk wanda ya soki gwamnati, ana daukarsa a matsayin dan ta'adda." Jaridar ta ce cafke wasu ma'aikatan kungiyar farar hula biyar, ya sabawa alkawarin da Shugaba Mnangagwa ya yi na dora kasar a bisa tsarin sassaucin ra'ayi. Cikin wannan makon ne aka cafke wasu masu adawa da gawamnati su biyar a kasar ta Zimbabuwe. An zargesu da shirya yi wa Shugaba Emmerson Mnangagwa juyin mulki. Jami'an 'yan sanda sun cafke mutanen a filin jirgin sama na Harare babban birnin kasar, yayin da suka dawo daga tafiya. Ana zarginsu da gudanar da taro domin shirya juyin mulki a kasar Maldives, da aka ce wata kungiyar farar hula ta kasar Sabiya ta shirya. Tun dai a karshen shekara ta 2017 ne Mnangagwa ya kama madafun iko a Zimbabuwe, biyo bayan ajiye mulki da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe da ya mulki Zimababuwe tsahon shekaru 37 ya yi sakamakon matsin lambar da ya fsukanta daga al'ummar kasar.