Afirka a jaridun Jamus
August 16, 2019A wannan makon sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka ya fara ne da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta duba cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango inda ta fara da cewa gwajin magungunan jinya sun fara yin kyakkyawan nasara sai dai har yanzu hakan ba ya nufin kawo karshen annobar Ebola a gabashin Kwango. Jaridar ta ce bayan labarai marasa dadin ji game da cutar ta Ebola a makonnin baya-bayan nan, yanzu akwai dalili na kyakkyawan fata, sakamakon nasasar da aka fara samu karkashin matakan gaggawa na wani binciken kimiyya da aka gudanar kan majinyata kimanin 700 da aka ba su maganin cutar Ebola, inda biyu daga cikin magungunan suka yi tasiri ta yadda nan gaba za a iya amfani da su wajen jinyar masu cutar Ebola. Jaridar ta ce wannan ka iya yin tasiri sosai a yakin da ake yi da annobar Ebola da kuma watakila wata annobar da za ta iya barkewa nan gaba. Sai dai duk wata alamar nasara da magungunan suka nuna ba za ta yi amfani ba matukar al’ummar da ake yi dominsu ba su bada hadin kai ba, inji jaridar.
'Kasar Kenyar da babu cin hanci da rashawa, abu ne mai yiwuwa', wannan shi ne taken labarin da jaridar Die Tageszeitung ta mayar da hankali akai, dangane da yankin Makueni da ke kudancin kasar Kenya. Jaridar ta ce gwamman jihar, Kivutha Kibwana na tafiyar da wata siyasa ta shigar da jama’a cikin ayyukan gwamnatinsa, abin da ke zama bakon abu a kasar ta Kenya inda yin sama da fadi da kudin kasa da cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare. Jaridar ta kara da cewa daga cikin hanyoyin da gwamnan ke bi sun hada da jin koken jama’a tare kuma tabbatar da cewa an aiwatar da dukkan ayyuka na ci-gaban yankin ba tare da an karkatar da kudaden da aka ware domin wadannan ayyuka ba zuwa wasu wurare na daban. Jaridar ta ce daukacin mazauna jihar sun gamsu da aikin gwamna Kivutha Kibwana, dan shekaru 65 wanda a 2013 ya lashe zabe karkashin lemar wata karamar jam’iyya a yankin, wanda kuma ya nisantar da kansa daga manyan jam’iyyun kasar.
Zubar da jini don tara abin duniya: nata taken kenan jaridar Neues Deutschland, inda ta kara da cewa kashe kananan yara don tsafi na zama sabon salon kasuwanci ga matsafa a nahiyar Afirka. Jaridar ta ba da misali da kasar Yuganda inda matsafa ke kashe kananan yara suna yi wa abokan huldarsu alkawuran samun arziki da koshin lafiya. Jaridar ta ce ko da yake babu alkalumman yawan yaran da wannan aikin rashin imani ya ritsa da su, amma a cikin shekaru 10 da suka gabata an sami karuwar yawan yaran da ake kashewa saboda tsafi. Ta ce kashi 85 cikin 100 na yawan al’ummar kasar; miliyan 40 a Yugandar Kiristoci ne, sannan kashi 15 cikin 100 na al'ummar ne kawai Musulmi, amma imanin samun wani matsayi ta hanyar tsafe-tsafe ya zama ruwan dare. Sai dai yanzu limaman Kirista da Musulunci sun tashi tsayin daka don yakar wannan ta’asa da ke da alaka da camfe-camfe. Jaridar ta ce tun bayan da shugabannin addinan biyu suka dauki matakan kare kananan yaran, kashe-kashen na tsafi sun ragu.