Shekaru 30 da hadarin nukiliya mafi muni
April 26, 2016Talla
A wannan Talata a Ukraine ana cika shekaru 30 da hadarin nukiliya mafi muni da duniya ta fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu da ya faru a Chernobyl abin da ya kai ga mutuwar dubban mutane, sannan ya janyo sake tunani kan yadda ake tafiyar da harkokin da suka shafi nukiliya.
Fiye da ton 200 na uranium ya fice daga cikin lalataccen abin da ake sarrafa nikiliya ya shafi sassan Turai, inda cikin kwanaki 10 ya haifar da wani mummunan sakamako.