1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta cika shekaru 55 na 'yanci da tulin kalubale

Ubale Musa/YBOctober 1, 2015

Ko bayan tuna ranar 'yancin kai a tsakanin kowa bikin har ila yau ya zamo dama ta siyasa ga jam'iyyar APC da tayi nasarar nuna hadin kai a tsakanin shugaban kasar da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

https://p.dw.com/p/1Gghv
Unabhängigkeitstag in Nigeria 2015
Shugaba Buhari a tsakiya tare da mukarrabansa lokacin yankan alkaki karo na 55 da samun 'yanciHoto: DW/U. Musa

Sun dai kau da ido ga jerin matsalolin rashin tsaro da barazana ta rushewar tattalin arziki, domin biki na cikar kasar shekaru 55 na 'yancin kai a bangaren mahukunta da manyan bakin da suka share sa'oi kusan uku suna biki a fadar gwamnatin tarrayar kasar ta Aso Rock.

Bikin kuma da ke zama irinsa na farko ga sabuwar gwamnatin da ke zaman irinta ta farko ta adawa da ta dau ragamar harkoki na kasar.

Tulin kalubale a gaban Najeriya

Duk da cewar dai har yanzu kasar tana tsakiya a ruwa a cikin jerin kalubale da ke barazana ga makomarta da ma kaita cikin manya na kasashe, a wani jawabinsa tun da sanyi na safiyar Alhamis dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar ta shawo kan matsalar Boko Haram da ke zaman mafi girma ga kasar tun da sanyin safiyar mulkin nata.

Unabhängigkeitstag in Nigeria 2015
Shugaba Buhari da Sanata Saraki na tattaunawa ranar bikin tuna samun 'yanciHoto: DW/U. Musa

“Sojojinmu masu kwazo karkashin sabon shugabancinsu sun kai yakin ya zuwa kofar 'yan gwagwarmaya, kuma sun lalata karfinsu gaba daya, Boko Haram sun tarwatse suna gudu a hallin yanzu. Kuma kai harinsu kan cibiyoyi na fararen hula irin na su sansanonin 'yan gudun hijira na zaman alamar tsoro a gare su. Na kuma umarci jami'an tsaro da al'ummar yankunan da su ci-gaba da sanya ido”.

Jawabin dai ya zamo damar farko ga shugaban na nuna irin nasarori na gwamnatin a watanin hudu, sannan da bukata ta hadin kai a tsakanin daukaci na 'yan kasa da nufin cika burin kowa.

Hadin kan shugabanni

Hadin kan kuma da ke zaman wa'azin masu ruwa da tsaki da bikin da ya samu halartar manyan 'yan kasar da ma bakinta.

Janaral Yakubu Gowon dai na zaman shugaban da ya jagoracin hadewar kasar zuwa wuri guda bayan yakin basasarta na farko.

Unabhängigkeitstag in Nigeria 2015
'Yan Najeriya na rawa a lokacin bikin tuna ranar 'yanciHoto: Reuters/A. Akinleye

Ko bayan tuna ranar 'yanci kai a tsakanin kowa bikin har ila yau ya zamo dama ta siyasa ga jam'iyyar APC da tayi nasarar nuna hadin kai a tsakanin shugaban kasar da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da suka dauki lokaci suna raha da annashuwa a karon farko.

Abun kuma da a fadar Sanata Ali Ndumu da ke zaman shugaban masu rinjaye na zaman alamar dinkewa a tsakanin sassan.

Bikin dai ya kuma zamo damar nazari a tsakanin tsofaffi da ma sabbabi na jami'ai na gwamnatin da suka kalli harba bindiga 21 da yankan alkaki na bikin da kuma sakin tattabaru na zaman lafiya ga 'yan kasa.

Admiral Murtala Nyako dai ya ga fari ya kuma hangi baki a cikin tafiyar kasar na shekaru 55, kuma a fadarsa ba'a tuna baya ga dan gyartai da ya samu sarauta a cikin rana.