Shekaru 60 a yanayin yaki da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
Jagoran adawa kuma mataimakin shugaban kasa a Sudan ta Kudu Riek Machar, a karshe ya sauka a Juba, abin da zai zama fata na aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a watan Agusta na 2015.
Sudan ta Kudu: An rika fafata yaki tun lokacin Turawan mulkin mallaka
Shekaru gwammai kasar Sudan ta Kudu ta kasance wani bangare na kasar Sudan, kokarin ballewarta daga kasar ta Sudan ya samo asali tun a shekarar 1955, tun ma kafin Turawan mulkin mallaka su mika yankin ga mahukuntan Khartoum, bangaren kudanci da ke zama na mabiya addinin Kirista na fafutikar samun 'yanci daga bangaren Larabawa da ke arewacin kasar.
Baraka tsakanin 'yan tawaye
Daga shekarar 1972 zuwa 1983 Sudan ta Kudu ta ga kwanciyar hankali kafin ta fada yakin basasa. Dakarun Sudan People's Liberation Movement and Army (SPLM/A) sun dauki kayan yaki bisa jagorancin John Garang. Daga baya 'yan tawayen suka rabu bisa jagorancin Salva Kiir da Riek Machar kowane na jan tawagarsa.
Samun 'yanci
A watan Janairu na shekarar 2011 an yi kuri'ar raba gardama inda al'umma a Sudan ta Kudu suka zabi samun 'yancin kai daga Sudan. Salva Kiir da Riek Machar suka zama shugaban kasa da mataimakinsa. An dai girka kasar bisa tubalin yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a 2005 karkashin jagora Garang, wanda ya rasu makonni bayan yarjejeniyar a wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu.
Sake daukar makamai
Kawancen abokan gabar dai bai je ko'ina ba, a watan Yulin 2013 shekaru biyu bayan samun 'yanci shugaba Salva Kiir ya kori Riek Machar da sauran ministocinsa. A watan Disamba ya bayyana da kayan soji lokacin ganawa da manema labarai inda ya zargi Machar da yunkurin juyin mulki, wannan shi ne dalilin komawa ruwa a yakin basasar da kasar ta sake shiga a baya-bayan nan.
Rikici mai muni
Akalla mutane dubu 50 ne suka rasu a rikicin duk da kokari na sulhu a karo daban-daban, mutane miliyan biyu da dubu 400 sun kaurace wa muhallansu. A watan Mayu na shekarar 2014 dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dubu 14 da ke a kasar sun karkata hankalinsu kan ba da kariya ga fararen hula. Kokarin samar da zaman lafiya da ke cikin kila-wa-kala.
Fata ya gushe
A watan Mayu na 2015 bayan ganawa tsakanin shugaba Kiir da Machar a Addis Ababa an cimma yarjejeniya da burin samar da zaman lafiya, sai dai wannan fata ya gushe bayan sa'o'i kadan inda aka sake komawa filin daga. Wasu yarjeniyoyi da aka cimma ma ba su je ko'ina ba. Abin bai tsaya tsakanin shugabannin ba a cewar masu sanya idanu, tsakanin magoya bayan nasu ma kai ya rabu.
Sake hadewar masu gaba da juna
Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a watan Agusta na 2015 ta fara da tangarda, da fari Shugaba Kiir ya ki amincewa da sanya hannu daga bisani ya amince bayan matsin lambar kasa da kasa. Cikin yarjejeniyar Machar zai dawo daga kasar Habasha da yake neman mafaka. Batun wadanda za su yi masa rakiya zuwa Juba dauke da makamai shi ne aka yi ta cece-ku-ce a kai.
Barnar da yakin basasa ke jawowa
Wannan yakin basasa dai ya daidaita kasar. Kwamishinan kare hakkin bil Adama a Majalisar Dinkin Duniya Said Raad al-Hussein, ya ce dukkanin bangarori na gwamnati da 'yan tawaye sun aikata fyade da ayyukan ta'addanci a lokacin yakin. Majalisar Dinkin Duniya dai ta shirya kafa wata hukuma da za ta binciki yakin da kasar ta fada.