1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyar da samun 'yancin kan Sudan ta Kudu

Waakhe Simon Wudu/ZLJuly 8, 2016

Matsin tattalin arziki ya sanya, kasar Sudan ta Kudu, soke bikin samun 'yancin kan kasar na cika shekaru biyar:

https://p.dw.com/p/1JLtp
Südsudan Referendum 2011
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Messara

Yarjejeniyar wanzan da zaman lafiyar da aka cimma a watan Aprilu wadda kuma ta haifar da sauyi, ta gaza habaka tattalin arzikin kasar da ya shiga rudu.Tun bayan da aka kafa gwamnatin hadin kan kasa a kasar Sudan ta Kudu cikin watan Aprilun, wannan shekarar a wani bangare na martaba yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya.Da dama daga cikin 'yan kasar ke da babban burin ganin sauyi a tattalin arzikin kasar; Sai dai za a iya cewar an samu daidaito tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar watanni biyu da suka gabata.

Tsadar rayu ta haddasa zaman kunci a kasar ta Sudan ta Kudu

Farashin kayayyakin bukatun yau da kullum sun yi tashin goran zabbi, ga misali, farashin sikari kilo guda ya kai fam 30 na kudin Sudan ta kudu, yayin da farashin fulawa kilo daya ya kai sama da fam 1,200.'Yan kasar ta Sudan ta Kudu na da ra'ayoyi masu cin karo da juna, kan soke bikin na bana, wani matashi Machael Atit ya ce shi kam bai ji dadi ba.

Südsudan Flüchtlingscamp Flüchtlinge in Yida
Hoto: Getty Images/AFP/A. G. Farran

"Soke bikin samun 'yancin kai abin takaici ne a matsayinmu na sabuwar kasa. Ba a gudanar da bikin bara ba yanzu kuma an ce ba za a yi ba, baya ga wannan kuma, ga rigingimu ga kuma matsalar tattalin arziki duk irin wannan ba zai haifar mana da kima a idanun duniya ba."

Matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da ita ta janyo sukar gwamnatin Salva Kiir

Bidali Aligo Samson, wani dan gwagwarmaya ne, na da ra'ayin cewa kudaden da za

Südsudan - Unterzeichnung des Friedensvertrags von Salva Kiir
Hoto: Reuters/J. Solomun

"Wannan yana da mahimmanci, na biyu kuma akwai abubuwa da yawa da yakamata a kyautata kamar batun ilimi da kyautatawa malaman makaranta da samar da yunifom, saboda haka bama bukata a kashe kudade a kan bikin rana daya."

Kasar Sudan ta Kudu dai ta samu 'yancin kai ne daga Sudan a shekarar 2011, bayan kwashe tsawon shekaru 20 ana gwabza rikici.