Yankin rainon Ingilishin Kamaru na cikin rikici
October 1, 2021Kumbo na kasar Kamaru ya fuskanci tarwatsewar bama-bamai shekarun da suka gabata, sakamakon rikin 'yan aware masu neman ballewa daga dunkulalliyar Kamaru da kuma sojojin gwamnati. Rashin tsaron a yankin masu magana da Turanbcin Ingilsihi a Kamaru, ya jefa rayuwar fararen hula cikin fagaba a kusan kullum tsakanin sojoji da kuma 'yan aware. Christabel mai shekaru 28 a duniya, har yanzu tana tuna baya, lokacin da sojoji suka farwa garin Kumbo da ke yankin Arewa mai nisa a Kamaru. "Wata rana na je gona don girbe kayan lambu bayan na zauna a cikin gida fiye da mako guda. A kan hanyata ta dawowa, na fahimci cewa akwai wuta ko'ina a cikin kwata. Mutum ba zai iya tantance ko wane gidaje ne ke ƙonewa ba. A wannan ranar, an kashe mutane biyar."
Karin Bayani: Kamaru: Mata na yajin cin abinci
Christabel, ta ce ba ta ma san inda 'yarta mai shekaru shida ta yi a loakcin da ta stere har tsawon kwanaki uku kamin suka sake haduwa da 'yar. Rikicin ya yi sanadiyyar kona gidan Christabel, matakin da ya sa ta komawa gidan jiya, gun mutumin da ta watsa wa kasa a ido bayan nuna sha'awar aurenta a baya. "Na samu labarin yana Yaounde tare da dan uwansa, Ba ni da wani zaɓi fiye da yarda da bukatarsa sa. Dole ne in bar 'yata tare da mahaifina kuma in tashi don Yaoundé don haduwa da saurayin. Na yarda da maganar aure saboda takaici kawai saboda ba ni da zabi. "
Karin Bayani: Matsalar mallakar fili a Kamaru
Yanzu haka ma'auratan yakamata a ce sun samu mafaka a Yaounde babban birbin kasar Kamarun, amma sai dai ryuwarda suka tsinci kai ba irin wacce suke fata ba. inji Christabel. "Kawunsa ne ke da gidan, babu wani wurin da za mu zauna dukkanmu, dole na kwantar da yata a kan dakali don mu samu wurin kwanciya, a hakan kuma na sake daukar wani sabon ciki kuma na yi rashin lafiya kuma ba shi da kuɗi ko kaɗan don kula da halin da nake ciki da kuma ɗaukar ciki a lokaci guda."
Yanzu haka rayuwar ta yi wa Christabel da mijinta daurin tam-tam, har yanzu mijinta na koyon tukin babbar mota, ita kuma tan talla a titunan Yaounde don samun na sawa a baka, sai dai abinda take samu bai taka kara ya karya ba. Christabel, daya ce cikin daruruwan mutanen da rikicin 'yan arawaren ya raba da matsugunasu, kuma yayin da rikicin ke shiga shekaru biyar ba tare da alamun dai-daito ba, akwai alamun jefa rayuwar fararen hula dama ciin mayuwacin hali.