Najeriya da Nijar: Shirin bikin Kirsimeti
December 22, 2023Yayin da 'yan mata ke zuwa wuraren yin kwalliya da gyaran fatar jiki cikin yanayin da kowa ke kokawa da tsadar kayayyaki sakamakon faduwar darajar Naira da hauhawar farashin kudin kasashen ketare da ke shafar harkokin kasuwancin Najeriya, a bangare guda samari na tserewa 'yan matan ne a irin wannan lokacin saboda tsadar rayuwar. Sai dai yayin da a Najeriyar ake kokawa da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin da kuma masassarar tattalin arziki, a makwabciyarta Jamhuriyar Nijar juyin mulkin da sojoji suka yi ne ya jefa al'umma cikin tasku.
Jim kadan bayan juyin mulkin ne dai, kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ta kakaba takunkumin mai zafi kan Nijar din. Sai dai wannan takunkumi ba wai sojojin da sukaa kifar da gwamnatin ya fi shafa kai tsaye ba, al'ummar kasar ne ke dandana kudarsu. Matsin tattalin arzikin da takunkuman suka haifar dai, ya sanya a bana mabiya Addinin Kirista a Jamhuriyar ta Nijar za su yi bukuwan Kirsimetin cikin halin tasku. Daga cikin matsalar takunkumin dai har da batun rufe kan iyakokin kasar, sai dai duk da wannan halin matsinmabiya Addinin Kirista a Nijar din sun kuduri aniyar yin adu'o'in samun sauki kan halin da kasar ke ciki.