1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ganawar yan Tawayen Taliban da jamián gwamnatin Koriya ta kudu

August 3, 2007

Tawagar koriya ta kudu na fatan yin ganawa kai tsaye da yan Taliban dake garkuwa da Koriyawa 21 domin samun masalaha ta sakin mutanen.

https://p.dw.com/p/Btup
Dangi da `yan uwan koriyawa da yan Taliban suka yi garkuwa da su a Afghanistan
Dangi da `yan uwan koriyawa da yan Taliban suka yi garkuwa da su a AfghanistanHoto: AP

Yan Taliban ɗin waɗanda suka amince suyi ganawar ta kai tsaye da jamián na Koriya ta kudun sun ce wajibi ne wurin da zaá yi ganawar ya kasance a yankin dake karkashin kulawar su. Kakakin ƙungiyar ta Taliban Qari Mohammed Yusif Ahmadi yace ba zasu amince da yin wata tattaunawa a yankin dake ƙarkashin gwamnatin Afghanistan ko kuma sansanoni na ƙungiyar tsaro ta NATO ba, domin a cewar sa basu amince musu ba, saboda ba mutane bane masu cika alƙawari. Yace a halin da ake ciki suna tattaunawa ta wayar tarho jakadan Koriya ta kudu.

Sai dai kuma a waje guda kakakin gwamnan lardin Ghazni Shireen Mangal yace har yanzu baá tsaida tartibin magana game da ganawar ba saboda an kasa cimma daidaito tsakanin tawagar koriya ta kudun da wakilan yan Taliban ɗin a game da wurin da ya kamata a yi tattaunawar.

Fadar gwamnatin Koriya ta kudun a birnin Seoul na fatan tattaunawar ta gaba da gaba zata cimma nasarar sakin koriyawan 21.

A ranar jumaár nan ne dai ake sa ran gudanar da tattaunawar tsakanin yan tawayen da tawagar koriya ta kudu ƙarkashin jagorancin jakadan koriya ta kudu a Afghanistan Kang Sung Zu. A ta bakin yan Majalisar dokokin Koriya ta kudu a Washington , Amurka bata fidda tsammanin yin amfani da karfin soji ba domin kwato mutanen da ake garkuwa da su. Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka a yankin kudu da kuma tsakiyar Asia Richard Boucher yace wajibi ne a cigaba da matsin lamba ga yan Taliban ɗin domin sakin Koriyawan.

Sai dai waɗannan kalamai na Boucher sun saɓa dana Ministan harkokin waje wanda yace Koriya ta kudu da Amurka ba za su yi amfani da ƙarfi ba wajen yanto mutanen da aka yi garkuwa da su.

A ranar Alhamis kakakin Taliban Qari Mohammed Yusuf Ahmadi yace sun yi tattaunawar sharar fage kai tsaye ta wayar tarho da jakadan na Koriya ta arewa Kang Sung Zu, yana mai cewa har yanzu suna nan a kan bakan su ta yin musayar koriyawan 21 da suke garkuwa da su da yan uwan su mutum takwas da ake tsare da su a gidan yari.

Sai dai rahotanni daga Seoul sun ruwaito jamián gwamnatin na cewa ba zasu iya cika wannan sharadi ba na sako fursunonin da gwamnatin Afghanistan ke tsare da su a gidan yari.

A ranar 19 ga watan Yulin da ya gabata yan Taliban suka kama koriyawan 23 waɗanda suka haɗa da mata 18 waɗanda ke tsakanin shekaru 20 zuwa 30 da haihuwa yayin da suke kan hanyar su daga Kabul zuwa birnin Kandahar a kudancin Afghanistan. Tuni dai yan Talin ɗin suka kashe maza biyu daga cikin Koriyawa.

Wata tawaga ta Pastocin coci sun gudanar da adduói na musamman a ƙofar ofishin jakadancin Amurka a birnin Seoul suna roƙon washington ta amince da buƙatun yan Taliban ɗin domin sakin waɗanda ake garkuwa da su. Maluman coci su 96 waɗanda suka sanya hannu a kan wata takarda sun baiyana cewa wajibi ne Amurka wadda ta hallaka mutane fararen hula waɗanda basu ji ba basu gani ba da sunan yaƙi da ayyukan taáddanci ta ɗauki nauyin da ya rataya a wuyan ta a game da wannan hali da Koriyawan ke ciki. A hannu guda kuma wata ƙungiyar musulmi a Indonesia ta yi tur da Allah wadai da garkuwar wanda tace ya saɓa da koyarwar addinin musulunci.