Shirin gwamnatin Najeriya na ƙayyade iyali
June 28, 2012Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyarta ta ɓullo da shirin ƙayyade yawan yaran da za'a baiwa magidanta izinin su haifa a cikin ƙasar, a wani mataki da ke haifar da taƙaddama a game da wannan batu mai sarƙaƙiyar gaske a yanayi irin na Najeriya. To ko me wannan manufa ke nufi ga Najeriya da take ƙasa mai cike da mabiya addinai da ƙabilu da dama?
Yunƙurin ɓullo da sabuwar manufar da za ta sanya 'yan Najeriya ƙayyade yawan yaran da gwamnati za ta basu izinin haihuwa da ke zama wani sabon babi da shugaban Najeriyar Goodluck Jonatahn ke tunkara, wanda ya bayyana aniyarsa ta yin hakan ta hanyar gabatar da ƙuduri a gaban majalisar dokokin Najeriyar domin neman amincewarsu.
Shugaban na Najeriya ya danganta bukatar yin hakan bisa dalilai na tabbatar da tsara manufofin ci gaban ƙasa, tuni ya hango irin taƙaddamar da wannan ka iya haifarwa da ya sanya shi fara yin gandagarki ga alu'mmar Najeriya Musulmi, Kristoci da ma waɗanda ke bin addinin gargajiya, yana mai cewa.
Kayyade iyali na da fa'ida ga tsara manufofin ci gaban ƙasa
"Kowace ƙasa tana taƙaita yawan al'ummarta, kuma a garemu idan har muna son gudanar da tsare tsare masu ma'ana to dole ne mu taƙaita yawan al'ummarmu, nasan wannan lamari ne mai sarƙaƙiya, ko ga Musulmi, Krista ko mabiya addinan gargajiya, domin 'ya'ya kyauta ce ta Allah, za'a ce bai kamata a ƙayyade yawansu ba, to amma mun san dole mu samu adadin da za mu iya kulawa da su biyu uku ko huɗu."
Sanin cewa wannan ne karon farko da ake yunƙurin ɓullo da wannan manufa a Najeriyar a daidai lokacin da ƙididdiga ke nuna adadin yawan al'ummar ƙasar da ya kai miliyan 162 ya sanya tambayar shin me ake nufi da ƙayyade yawan alu'mma ne bisa tsarin kula da al'umma. Dr Zaba Mohammed Yawa kwararren likita ne da ke Abuja.
Shirin ƙayyade iyali ka iya yin cikas ga allurar Polio
Koda yake wannan lamari ne da ke cike da sarƙaƙiya musamman ga al'umma irin ta Najeriya da a baya aka sha daga da ita a game da batun allurar rigakafi, balle a yi magana ta taƙaita yawan yaran da za'a baiwa mutane izinin haihuwa. To sai dai ga masana a fanin harkokin ci gaban ƙasa na wa lamarin kalo da ma fassara a wasu fannoni na daban kamar yadda Dr. Dauda Sulaiman Dauda, daraktan hukumar ƙasa da ƙasa mai kula da manufofin ci gaba ta Future Groups ya bayyana.
Najeriya dai ce ƙasa da tafi kowace yawan al'umma a nahiyar Afirka wacce hasashe ya nuna cewa nan da shekara ta 2050 za ta kasance ƙasa ta huɗu mai yawan alu'mma a duniya. Koda yake ana wa yawan jama'a kallon abin alfahari a ƙasar to sai dai ƙaulabalen koma bayan rayuwa da ake fuskanta na ƙara jefa tunani da ma sauyin rayuwa ga wasu rukunin jama'a da ke rungumar kaucewa haihuwar 'ya'ya yuu domin samu kwararar a tsarin rayuwarsu.
Abin jira a gani shine yadda za ta kaya a kan wannan yunƙuri da gwamnati ta sa a gaba na taƙaita yawan yaran da za'a baiwa magidanta haihuwa a cikin ƙasar, batun da tuni ya haifar da taƙaddama da ma ta da jijiyar wuya.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal