Shirin IS na kai hare-hare a Turkiyya
February 19, 2015Talla
Kafafen watsa labaran Turkiyya din sun rawaito hukumar leken asirin kasar na cewar dubban 'yan IS din na kokarin shiga kasar ta kudanci domin kame wasu yankuna da nufin maida su karkashin ikonsu da ma aiwatar da hare-hare.
Baya ga wannan, kafofin watsa labaran sun kuma ce akwai yiwuwar 'yan kungiyar ta IS din su danna cikin kasashe irinsu Bulgariya da makamantansu don kaddamar da hare-hare a wasu kasashen dake cikin kungiyar tarayyar Turai.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kawacen da sojin Amirka ke jagoranta ke cigaba da kai hare-hare kan mayakan IS din da nufin karya kashin bayansu.