1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Jamus na yaki da kwararar 'yan cirani daga Afirka

Abdourahmane Hassane/GATAugust 10, 2016

Ministan ma'aikatar hadin kan tattalin arziki da raya kasa na Jamus Gerd Müller na wani rangadi a wasu kasashen Afirka ta Yamma a wani mataki na shirin kaddamar da wani shiri na kawo karshen ci ranin 'yan Afirka a Turai

https://p.dw.com/p/1JfUt
Niger Agadez Sahara Flüchtlinge
Hoto: Reuters/Akintunde Akinleye

Ministan ma'aikatar hadin kan tattalin arziki da raya kasa na Jamus Gerd Müller gabannin tashinsa zuwa kasashen Senegal da Nijar ya yi gargadin cewar dole ne sai an girka tsarin Plan Marshall wajen yaki da kwararar 'yan ci rani zuwa nahiyar Turai, irin wanda aka yi amfani da shi bayan yakin duniya na biyu domin sake gina Turai. Müller wanda yanzu haka yake ci gaba da yin ziyarar aiki a Nijar bayan ya fito daga Senegal ya bayyana haka ne ga jaridar Bild am Sonntag.

Tsarin na Plan Marshall wanda Gerd Müller ke yin magana a kansa wanda aka yi amfani da shi wajen sake gina nahiyar Turai bayan yakin duniya na biyu,an rattaba hannu a kansa ne a cikin watan Satumba na shekara ta 1947, wanda ya tanadi cewar Amirka ta ba da taimako na biliyoyin dalalolin a matsayin rance ga kasashe 23 na Turai wadanda aka ragargaza a lokacin yakin duniya na biyu domin sake gina kasashensu.

Müller ya ce idan har ana son a kawo karshen lamarin na kwararar baki 'yan ci rani galibi matasa, sai kasashen yammacin duniya sun ba da himma wajen saka jari a nahiyar Afirka a tsawon shekaru da dama, tare da samun wata dama daga gwamnatocin na Afirka domin yin sassauci ga kudaden haraji misali a cikin fanonin kirkiro masana'antu irin na kare muhalli don samar da aiyyukan yi ga matasa.

Gerd Müller
Hoto: picture-alliance/dpa/E. Elsner

A lokacin da yake magana da manema labarai bayan ganawarsa da Shugaba Macky Sall na Senegal, ministan ma'aikatar hadin kan tattalin arziki da raya kasa na Jamus Gerd Müller ya sanar da tsarin taimaka wa kasashen na Afirka

"Dole mu tabbatar da kirkiro guraben aikin yi a kasashen Afirka. Senegal ta zama kasar da 'yan gudun hijira da ke son zuwa Jamus ci-rani, suke yada zango a cikinta. Sakonmu a nan shi ne makomarku nan a kasashenku, saboda haka muke zuba jari mai yawa a Senegal da Nijar da ma sauran kasashen Afirka."

Misali dai a zance da ake yi Jamus ta ware karin kudi Euro miliyan 10 don habaka aiyyukan hadin kai da Senegal. Wanda ke zaman na dakatar da tudadar 'yan ci ranin zuwa Turai akasari ma matasan da ke da sha'awar zuwa ci rani daga Senegal zuwa jamus.

Manazarta dai irinsu Farfesa Mageuye Kasse malami a jami'ar Cheik Anta Diop da ke a birnin Dakar wanda ya kware a kan sanin al'amuran hulda tsakanin Jamus da kasashen Afirka ya yi furcin cewar

''Wannan ziyara ta ministan na Jamus ta kara fadikar da jama'a musamman ma kungiyoyin mata da matasa a game da irin matakan da za a dauka a kan batun ko ma baya ga tsarin Plan Marshal

Da yawa dai daga cikin masu yin fashi bakin a kan al'amura na ganin cewar yana da mahimmanci a hada da kamfanoni masu zaman kansu a game da wannan tsari da ake son kaddamarwa idan har ana son al'umma ta ci moriyar shirin a cewar Mouhamadou Mbodji shugaban kwamitin hadin gwiwa na African Forum da ke a Dakar sannan kuma ya kara da cewa.

Italien Flüchtlinge aus Libyen gerettet
Hoto: Getty Images/AFP/G. Isolino

'' sai an hada da wakilai na kungiyoyin farar hula a cikin irin wannan tsari tattare da ba da kwarin gwiwa ga jama'a domin halarta wannan tattaunawa ya ce idan kawai tsari da za a yi tare da shugabannin ya ce hakan zai kara karfafa hanyoyin cin hancin da karbar rashawa.''

Daman dai a watan Disamba da ya gabata Gerd Müller ya ba da irin wannan shawara ta kafa tsarin Plan Marshall domin ceto kasahen Iraki da Siriya, amma ba tare da samun wani martani ba. Sai dai masu lura d al'amura na ganin cewar watakila idan har aka tabbatar wajen ganin an yi amfani da wannan tsari domin taimaka wa nahiyar Afirka, ba mamaki a samu saukin ficewar matasa daga nahiyar Afirka domin zuwa ci rani a nahiyar Turai.