Shirin kafa gwamnati a Isra'ila
April 10, 2019Talla
Shugaban Isra'ilar Reuven Rivlin, ya ce zai soma tuntubar 'yan siyasar kasar da suka yi nasara, don fara tsara dabarun kafa sabuwar gwamnati a makon gobe.
Shugaban ya ce za a watsa ganawar da zai yi da 'yan siyasar ne kai tsaye ta kafafen watsa labarai da jama'a ke amfani da su a kasar.
A cewarsa hakan ne zai tabbatar da baza komai a faifai, kamar yadda wata sanarwar da ya fitar ta nunar.
Bayan sauraron dukkanin shawarwarin da bangarorin za su iya bayarwa kan firaminista na gaba, shugaban na Isra'ila zai bayyana dan majalisa da za a dora wa nauyin kafa gwamnatin.
Tuni dai shugabannin kasashe suka yi nisa wajen yi wa Firamnistan Isra'ilar Benjamin Netanyahu tayin murnar nasara a zaben da aka kammala.