A cikin shirin za a ji cewar shugaban Amirka Donald Trump ya ce akwai yiwuwar ya sake ganawa da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un. Yan sanda a Isra'ila sun bukaci tuhumar firaministan kasar Benjamin Netanyahu kan zargin cin hanci. Muna kuma tafe da shirin Afirka a mako da Abu Namu da Ku shiga kulob da kuma zabi sonka.