Baya ga labaran duniya, a cikin shirin za a ji cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a yankin Bosso na jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar inda suka hallaka sojoji 32 da jikkata wasu da dama. A Najeriya kuwa gwamnatin kasar ce ta bayyana adadin kudin da ta kwato da hannun wanda ake zargi da yin sama da fadi da dukiyar kasa.