Cikin shirin za a ji cewa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kiran a gudanar da sahihin bincike kan kisan dan jaridan nan Jamal Khashoggi, yana mai jaddada cewa lallai ne a hukunta duk wani da aka samu da laifin kisan da aka yi a farkon watan Oktoba.