A kokarin magance boren ganin bayan mulkin soji dake ci gaba da ruruwa a Sudan, Shugaban sojin kasar Janar Abdel Fatah al-Burhan, ya sanar da kafa sabuwar majalisar rikon kwarya da ta kunshi sojoji da farar hula inda ya sake nada kansa a matsayin shugaban riko.