A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya, ana hasashen cewa ta yiwu siyasar kabilanci ta bulla a babban zaben shekarar badi. A Jamhuriya Nijar, al'umma ne ke kokawa kan karin farashin man diesel da ma karancinsa, lamarin da haifar da karin wahalhalu na rayuwa.