A cikin shirin za ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Zamfara ta kwace mulki daga hannun APC, bayan da hukumar zaben jihar ta ayyana Dauda Lawan Dare a matsayin wanda zai dafa madafan iko. Masu sa ido a zaben gwamnonin Najeriya sun koka kan abinda suka kira ba wa masu zabe na toshiyar baki don sayen kuri’u a yayin zaben da ya gabata