Cikin shirin za a ji cewa hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta kyautata wa 'yan hijirar da ke a kasarta. Wannan kira ya dai dai da lokacin da 'yan zaman hijira daga ketare ke kokawa da halin da suke ciki a Najeriyar.