Firaministar Birtaniya Theresa May za ta fuskanci kuri’ar rashin amanna bayan da majalisar dokoki ta yi watsi da shirinta na ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai. Gwamnatin Kenya ta shawo kan harin da wasu yan bindiga suka kai wani otel a Nairobi babban birnin kasar.