Cikin shirin za a ji hukumomin a Zimbabuwe sun damke shugaban jami'ar kasar da aka yi zargin ya bai wa matar tsohon shugaba Robert Mugabe wato Grace Mugabe digirin digirgir na boge. Masu bincike a hukumar dake yaki da almundahana a kasar, sun ce shugaban jami'ar Farfesa Levi Nyagura, yana sane da bai wa Grace Mugabe digirin, bayan 'yan karatu wasu 'yan watanni kacal.