Cikin shirn za aji sharhin da ya nuna damuwa da gwanjon bakin haure 'yan Afirka a kasar Libya, abin da ya nuna yadda ake kaskantar da dan Adam tare da cin mutuncinsa. Sahrhin ya ce dole ne a yi tir da Allah wadai da dukkan nau'o'i na akidoji da nuna wariya da ke kaskantar da mutane ya zuwa wata hajoji da za a iya kaiwa kasuwa a yi gwanjonsu.