Baya ga labaran duniya wanda ya tabo batun zaben shugaban kasa a kasar Tanzaniya, shirin ya kunshi rahotanni ciki kuwa har da martanin da mutane ke maidawa kan soke zaben gwamnan jihar Rivers da ke yankin Niger Delta na Najeriya wanda kotun saurarar karar zabe ta yi a kasar. Akwai kuma sauran rahotanni da kuma sharhuna na jaridun Jamus kan nahiyar Afirka.