A cikin shirin za a ji cewa yau ake sa ran Firaiministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya aiwatar da shirinsa na mamaye kaso 30 cikin 100 na yammacin kogin Jordan, matakin da ka iya ja wa Falasdinawa babbar asarar karfin iko da suke da shi a yankin. A Tarayyar Najeriya kuwa darurruwan matasa ne suka fara tururuwa don rejistar sunayensu a tsarin nan na bada tallafi da horon kan sano’i wato N Power.