A cikin shirin za a ji cewa Kasar Masar da Sudan sun cimma sabbin yarjeniyoyin kasuwanci da na tsaro, a daidai lokacin da batun madatsar ruwan Nilu da Habasha ta yi gaban kanta ke ta da hankalin shuwagabanin kasashen. A Najeriyar matsalar killace matasa da ake zargin ko dai suna shaye-shaye ko kuma suna yin wata gaggara na ci gaba da zama ruwan dare a yankin arewacin kasar.