A cikin shirin za ku ji ana shirin fara sauraran shari'ar kisan bakar fatar nan na Amirka George Floyd. Akwai rahoto a game da yadda caji ofis na 'yan sanda ke fuskantar hare-hare a kudancin Najeriya da rahoto a kan buhunan tabar-wiwin da Jamhuriyar Nijar ta kama da sauran wasu rahotanni.