A cikin shirin za ku ji sojoji sun yi wa firaministan Sudan ''kamun talala'' a wani mataki da wasu ke cewa juyin mulki ne aka yi. Akwai rahoto kan yadda fataucin miyagun kwayoyi ke yi wa Najeriya barazana. Muna tafe da rahoto kan korafin matasan Ghana kan yadda suka zargi gwamnati da sanya musu haraji fiye da kima a harkokin kasuwanci.