A cikin shirin za a ji cewa, Najeriya na son kafafen sada zumunta na zamani su rika bata bayanai na mutanen da ake zargin ka iya zama barazana ga rayuwar al'umma. A Nijar kuma wasu kungiyoyin fararen hula ne suka gudanar da taron wayar da kan al'umma kan mahimmancin bibiyar kasafin kudin kasa.