Cikin shirin za a ji halin da ake ciki a Sudan, musamman kan yarjejeniyar zaman lafiya da za a yi a Saudiyya. A Kwango asarar rayuka aka yi ta sama da mutum 200 sakamakon ambaliya. A Jamhuriyar Nijar kuwa kokari ake yi na duba rawar da mata za su taka ta bangaren tsaro da zaman lafiya a Sahel.