A cikin shirin akwai tsananin tabarbarewar halin jinkai a kasar Sudan da yadda iyalai 'yan hijira ke ciki a jihar Kaduna da ke Najeriya da yadda aikin ciyar da yara a makarantun firmare yake a Najeriyar. A Nijar ma batun masu tsere wa gidajensu a Tillaberi. Ghana kuma na fama ne da matsalar daukewar wutar lantarki.