A ciki akwai kokari da hukumomin lafiya da wasu kungiyoyi suke yi a Nijar a bangaren fadakar da jama'a kan cutar yoyon fitsari. Kamfanonin jigilar Alhazai kuwa a Nijar din ba su ji dadin wajen ajiye maniyattan kasar ba a Saudiyya. A Najeriya an yi karin kudi ga maniyyata a bana saboda yakin kasar Sudan.