Shirin ya kunshi zargin yunkurin juyin mulki a Rasha. Da matsalolin da masu bukata ta musamman ke gani bayan janye tallafin man fetir a Najeriya. 'Yan jihar Katsina na korafi kan nade-naden manyan sakatarorin gwamnati da gwamnan jihar ya yi. A Nijar kuwa matasa ne suka soma kintsa wa shagulgulan naman Sallar Layya.