Za kuji cewar jakadun kasashen Turai da yawansu yakai Ashirin sun yi kira ga gwamnatin kasar Chaina da ta kawo karshen tsare 'yan kabilar Ouighour dake yankin Xinjiang na kasar, cikin wata budaddiyar wasika da suka aikewa Coly Seck shugaban hukumar kare hakkin bil 'Adama a Majalisar Dinkin Duniya.