Za kuji cewar Jagororin Zanga-zanga a kasar Sudan sun amince da zabar Abdallah Hamdok tsohon jami'in Majalisar Dinkin Duniya a matsayin Firaministan kasar na farko, wanda kuma zai jagoranci kasar har na tsawo shekaru uku bayan an kai ruwa rana tsakaninsu da sojojin da suka hambarar da tsohuwar gwamnati.