Afirka: Kokarin kafa fasahar sararin samaniya
April 21, 2023Nahiyar Afirka ta jima da samun koma baya a fannin samar da tauraron dan adam a shekarun baya, ko da shi ke nahiyar ta fara samun ci gaba, in ji masana. Dama dai tattalin arzikin da ya shafi sararin samaniya yana daya daga cikin masana'antun fasaha mafi girma a duniya, saboda haka ne Kungiyar Tarayyar Afirka ta shirya taro kan fasahar sararin samaniya a birnin Abidjan na Cote d' Ivoire har zuwa 28 ga watan Afirlu.
Masana sun nunar da cewar akwai kyakyawar dama ga Afirka na iya kafa masana'antar fasahar sararin samaniya nan ba da dadewa ba, lamarin da zai taimakawa al'ummar wannan nahiya. Ya zuwa yanzu, an harba dukkan tauraron dan adam na Afirka daga wajen nahiyar Afirka saboda ba ta da wuraren harba tauraron. Amma nan ba da jimawa ba nahiyar za ta canza salon kamun ludayinta, inda gwamnatocin Afirka da yawa sukea zuba hannun jari a fasahar sararin samaniya, baya ga 'yan kasuwa daga ko'ina cikin duniya da ke bin sahun, wajen zuba jari.
A shekarar 2021 darajar masana'antar fasahar sararin samaniya ta Afirka ta kai kusan dalar Amirka biliyan 20. Alhali nan da shekarar 2026, ana sa ran wannan darajar za ta haura zuwa kusan biliyan 23. A halin yanzu, Afirka tana da kamfanoni sama da 270 a fannin fasahohin sararin samaniya a fannonin da suka hada da sadarwa da tsaro, jigilar kayayyaki da sufurin jiragen sama da hakar ma'adinai da noma da ilimi da lafiya.
An riga an shirya tashar fasahar sararin samaniya ta farko a Afirka a Djibouti, a yankin Kahon Afirka. A farkon wannan shekarar ne aka rattaba hannu kan wata sanarwar fahimtar juna tsakanin shugaban kasar Djibouti, Isma'il Omar Guelleh, da kamfanin fasahar sararin samaniya na Hong Kong na kasar Sin. Wannan tashar da za a kashe dalar Amirka biliyan daya wajen gina ta cikin shekaru biyar, Djibouti za ta samu karfin yin amfani da mashigin tekun Bahar Maliya, wanda ke da matukar amfani a fannin kasuwanci da jigilar kayayyaki a duniya.
Ita ma Kenya taurarinta ya haska bayan da ta gudanar da wani gagarumin aiki a fannin sararin samaniya ta hanyar harba tauraron dan adam na farko da ake wa lakabi da Taifa-1, wanda wata tawagar masu bincike na kasar suka tsara. Amma daga California na Amirka ne aka harba Taifa-1 zuwa sararin samaniya. Ana sa ran Taifa-1 za ta samar da bayanan kula da aikin gona da muhalli a Kenya, lamura masu kima ga makomar kasar da ke gabashin Afirka da ke fama da fari a halin yanzu.
A watan Oktoba 2022, Angola ta harba tauraron dan adam na biyu a sararin samaniya, mai suna Angosat-2, mai nauyin ton biyu da karfin isar da bayanai. Tauraron dan Adam din da ya kai dala 320, an gina shi ne a kasar Rasha kuma an harba shi daga kasar Kazakhstan. Dama gwamnatin Angola ta yi alkawarin sanya kasar a kan gaba a fannin sadarwa a nahiyar Afirka.
Ba a wai a Angola da Kenya ko Djibouti ne kawai ake ganin wannan ci gaba fasahar sararin samaniya ba, amma a ko'ina cikin Afirka, misali a Afirka ta Kudu ko Najeriya, inda ake smun matasa masu bincike suke kara cudanya a duniya tare da yin aiki tare da Amirkawa da Turawa da Rashawa da 'yan Chaina don samun kwarewa a fannin sararin samniya.