Shirin sanyawa Sudan ta Kudu takunkumi
September 5, 2015Talla
Jakadar Amirka da ke Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power ta shaidawa kwamitin sulhun Majalisar ta Dinkin Duniya cewa su na shirin kakaba takunkumi kan mutum biyu a Sudan ta Kudu din ne.
Ms Power ta ce mutum guda daga cikin mutanen biyu ya na bangaren gwamnati ne yayin da cikon gudan ke bangaren 'yan tawayen da ke zaman doya da manja da gwamnati shugaba Salva Kiir.
Wannan takunkumi da ake shirin kakabawa dai zai hada da haramta tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya da hana taba kadara da kuma haramtawa wanda aka sanyawa din sayen makamai.