Za a yi amfani da dokar kasa da kasa kan Carles Puigdemont
March 9, 2021Majalisar tarayyar Turai ta bayar da damar tasa keyar tsohon Shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont kasarsa ta asali don fuskantar shari'a, wannan na zuwa ne bayan umarnin majalisar na janye rigar kariyarsa wanda ake bai wa 'yan majalisun kasashen Turai. Tuni gwamnatin Spaniya ta baiyana gamsuwarta da matakin da ta ce nasara ce babba da za ta bayar da damar tuhumar wanda yayi yunkurin raba kasar gida biyu.
A nasa bangaren, Puigdemont da ke gudun hijira yanzu haka a kasar Beljiyam, ya baiyana takaici kan matakin Tarayyar Turai. A shekarar 2017, jagoran 'yan awaren na yankin Kataloniyan ya jagoranci ballewar yankin daga kasar Spaniya a abinda ya kira gwagwarmayar kwatar 'yancin yankin. Daga bisani ya tsere daga kasar inda ya nemi mafaka a kasar Beljiyum, mahukuntan kasar Spaniya ba su da 'yancin cafke shi bisa rigar kariyarsa amma da wannan matakin, 'yan sandan kasa da kasa za su yi aiikinsu na kama shi tare da mika shi hannun hukumomin Spaniyan. Ana tuhumarsa da wasu mukarrabansa da laifuka na cin amanar kasa da kuma almundahana.