Shirin toshe shafukan sada zumunta a Kwango
December 15, 2016Talla
Yayin wani zaman taro da hukumar sadarwa ta kasar ta Kwango wato ARPTC ta gudanar tare da wakillan kamfanoni hudu na wayar sadarwa a kasar ta sanar da su wannan mataki. Hukumar sadarwar ta kuma ce, idan har daya daga cikin kamfanonin ya ki bin wannan umarni, to zai fuskanci fushinta, inda za ta kai a dakatar da izininsa na gudanar da ayyuka a kasar. Shafukan sadarwan da za a toshe sun hada da na Facebook, da WhatsApp, da Twitter da dai sauran su, inda za a dakatar da su a ranar Lahadi 18 ga watan Disamba daga bakin karfe 18 na yamma 'yan awoyi kafin karshen wa'adin mulkin Shugaba Kabila.