Cikin shirin za a ji cewa shugaban kasar Laberiya ya ziyarci Najeriya yayin da a Jamhuriyar Nijar majalisar dokokin kasar ta koma aiki bayan hutun watanni uku da 'yan majalisar suka yi. Batutuwan da majalisar ta duba dai, sun hada ne da matsalar karancin abinci da aka lura ke kokarin zama babban batu da kuma dokar kasafin kudin kasar ta bana.